Iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, sun sanya ranar 23 ga watan Fabrairu a matsayin ranar binne shi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalan marigayin suka fitar a shirye-shiryen binne marigayin mai dauke da sa hannun babban dansa, Oluwarotimi Akeredolu, a Ondo ranar Litinin.
Karanta wannan: Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu
Marigayi Akeredolu ya rasu ne a ranar 27 ga watan Disambar 2023 a wani asibitin kasar Jamus sakamakon doguwar jinya.
Karanta wannan: Kotu Ta Dakatar Da Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar Ondo
Sanarwar ta bayyana cewa za a fara gudanar da jana’izar ne tun daga ranar 15 zuwa 25 ga watan Fabrairun 2024, a Ibadan da Akure da Owo kuma za a binne shi a garin kakaninsa wato Owo.