
A ranar Litinin ne Shugaban Kamfanin A.A Rano Nigeria Limited, Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Maryam Shekarau, ya kaddamar da sabon ginin karbar magani a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH).
A yayin kaddamar da ginin katafaren ginin da Sanata Ibrahim Shekarau ya gina, AA Rano wanda Alhaji Salisu Ibrahim Balarabe ya wakilta ya bayyana ginin a matsayin wani aiki da zai yi wa al’umma.
Ya kuma yi kira ga mahukuntan asibitin da su yi amfani da shi yadda ya kamata.
“Wannan gini, na sani zai taimaka matuka wajen taimakon mutane, amma sai an yi da yawa. Kulawa yana ɗaya daga cikin mahimman abubuwan da ke taimakawa wurin zama cikin tsabta, ba tare da lalacewa ba. Ina kira ga mahukuntan asibitin da ma’aikatan da za su yi aiki a nan da su kula da shi sosai domin ya cim ma manufarsa,” inji Rano.
Karanta wannan: Naira ta karu a kasuwar canjin kudade
“Har ila yau, ina so in yi amfani da wannan dama domin in gode wa mai girma, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, da ya kawo mana wannan aikin na ci gaban jiharmu. Allah Ya saka masa da alheri.”
A jawabinsa na maraba, Babban Daraktan Likitoci, Farfesa Abdurrahamn Abba Sheshe, ya ce aikin wani bangare ne na ayyukan mazabar Shekarau, wanda ya fara a shekarar 2021.
Karanta wannan: Iyalan marigayi Akeredolu sun sanar da ranar Jana’izarsa
“Tsohon rukunin ginin karbar maganin da muke da shi yayi ƙanƙanta ne kuma ga cunkoso. Don haka ne ma muka nemi Sanata Shekarau da ya zo ya gina mana wannan bangaren, domin ya zama kari ga tsohon da muke da shi.
Aikin yana daya daga cikin ayyukan jadawalin Shekarau, wanda ya fara a shekarar 2021, kuma a yau muka kaddamar da shi. Hakika ya yi wa ginin tanadin kayan aiki masu kyau domin mu samu walwala yanda ya kamata.”
Karanta wannan: Amurka da Burtaniya sun kara kai hari kan mayakan Houthi
A nasa jawabin, Sanata Malam Ibrahim Shekarau ya ce inganta harkokin kiwon lafiya na daya daga cikin abubuwan da ya sa a gaba, kuma ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen yin duk wani abu da zai inganta fannin.
“Lokacin da na tsinci kaina a matsayin mamba a kwamitin lafiya a Majalisar Dokoki ta kasa, na shaida wa kaina cewa wannan wata babbar dama ce ta zinare a gare ni na kawo ci gaba mai yawa ga jihata ta bangaren kiwon lafiya, domin na daya daga cikin bangarorin da suka fi ba ni fifiko.
“Haka kuma zan yi duk abin da zan iya domin inganta shi. A matsayinka na jagora, idan ba za ka iya kare rayukan ‘yan kasa ba, ka ba su ilimi mai inganci, kana kuma ba ka samar da ingantaccen kiwon lafiya a gare su ba, to ba ka da wani amfani.”
Karanta wannan: “Mu muka karɓo yaranmu daga hannun masu garkuwa da mutane, ba ƴansanda ba” – Sheriff Al-Kadriyah
“A tsawon lokacin da na yi a majalisar dokokin kasar, na yi ayyuka da dama a fannin ilimi. Mun gina tubalan da yawa a makarantu, kuma a bangaren lafiya ma mun yi ayyuka da yawa. Kuma ko da a yau mun zo ne don kaddamar da daya daga cikin gine-ginen da muka gina a bangaren lafiya.”
“Wannan wurin ana kiran sunan mahaifiyata. Ina so ku sani ba ni da hannu a cikin wannan. Ma’aikatan asibitin sune suka dage cewa suna son sakawa mahaifiyata suna. Na yi ƙoƙari na ƙi ra’ayin amma sun rinjaye ni.”
“Ko da kasancewa ta a nan, CMD ne ya dage cewa ya kamata in kasance cikin bikin. Idan ba haka ba, da ban kasance a nan ba. Amma duk da haka, a madadin iyalaina ina mika godiyata ga mahukuntan wannan asibitin da suka karrama ni ta hanyar sanya wa wannan wuri sunan mahaifiyata.”