ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da yunkurin hana matasa samun ilimi a Kasar nan

ASUU ASUU NEW
ASUU ASUU NEW

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da yunkurin hana matasan Najeriya samun ilimi mai inganci da gangan.

Kungiyar ta ce dukkan abubuwan da gwamnati ke yi sun bayyana karara cewa an dauki matakan lalata ilimi gaba daya a kasar musamman makarantun gaba da sakandare.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kungiyar ASUU reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano dake garin Wudil ta fitar a ranar talata dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar ASUU reshen Jami’ar Muhammad Sani Gaya da Sakataren Kungiyar Murtala Muhammad.

Sanarwar ta ce, ”Mun shirya kuma mun kuduri aniyar ci gaba da gwagwarmayar kawo karshen bautar damu domin mu samarwa kanmu da matasa da sauran al’ummomin da ke Najeriya daga kokarin da gwamnati ke yi na hana su samun ingantaccen ilimi mai araha.

“Abin takaicin shi ne, Gwamnatin Tarayya ta na da isassun mataimakan da ba su dace ba a wuraren da aka saka su domin kula da shi. Abin takaicin shi ne Ministan Ilimi, Adamu Adamu bai fahimci yadda tsarin jami’a da Kuma muhimman ayyukan malaman jami’a ba, al’umma na iya lura da hakan, bisa la’akhari da dokokin da suka kafa jami’o’i, ana daukar ma’aikatan ilimi aiki don koyarwa da gudanar da bincike tare da ayyukan ci gaban al’umma, don haka a lokacin da ASUU ta shiga yajin aikin sai kawai bangaren koyarwa ya daina aiki don haka sai aka bullo da batun “in ba aiki babu albashi” Wanda hakan bai dace ba kuma baya bisa doka ga ma’aikatan ilimi.”

A cewar sanarwar, bukatun kungiyar ba na son rai ba ne, illa son kawo gyara.

“A matsayin kungiyarmu ta masu ilimi da hankali, ta bukaci a mayar da jami’o’inmu masu matsayi domin samun ingantaccen ci gaban kasa da ci gaban fasaha.

“Har ila yau, a Samar makudan kudade masu dorewa ga jami’o’inmu; a gyatta koma baya da tsarin jami’o’i ya samu; da kuma, karin albashi ga ma’aikatan ilimi a Jami’o’in Nijeriya.

“Ya kamata ‘yan Najeriya su marawa kungiyar ASUU baya domin rokon gwamnatin tarayya da ta bi tafarkin karramawa ta hanyar mutunta yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar mu cikin karamci.”

Abin takaici ne a lura cewa yayin da gwamnati ta amince da bukatun ASUU a matsayin na gaske kuma na kishin kasa, amma duk da haka gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Manjo Janar Muhammadu Buhari ta nuna rashin martaba siyasa da rashin kishin kasa da karancin kudirin ceto tsarin Jami’o’i daga durkushewa.

Sanarwar ta ce: ‘Tsarin Ziyara’: – Dangane da dokar kawo sauye-sauye a Jami’o’i daban-daban (Tanade-tanade) dokokin da suka kafa jami’o’i da aka yiwa gyaran fuska a Shekarar 2003, ya bada damar ziyartar jami’o’in duk bayan shekaru biyar. An baiwa kwamitin ikon yin nazari da tantance ayyukan ilimi da kudi da Kuma gudanarwar jami’o’i da mika rahoto ga mai ziyara (La Allah Shugaban Kasa ga Jami’o’in Gwamnatin Tarayya ko Gwamnonin Jihohi ga Jami’o’in Jiha).

‘’Kungiyar ASUU reshen Jami’ar Wudil na son fayyace komai dalla-dalla cewa zarge-zargen da ake ta yadawa na cewa yajin aikin na watanni shida Jami’o’in Tarayya da gwamnati ne ke amfanuwa da shi, karya ne kuma dole a yi watsi da zantukan. Yana da kyau a bayyana cewa bukatun da aka ambata kai tsaye zasu amfanar da Jami’o’in Jihohi kamar yadda zasu amfanar da Jami’o’in Tarayya.’’

“Ta fuskar Manyan ayyuka dole ne a sanar cewa, Jami’o’in Jihohi sun dogara kacokan kan asusun tallafawa ilimin makarantun gaba da Sakandare wato TetFund da wasu ayyukan da makarantun ke bukata, wadanda dukkan su sakamakon gwagwarmayar Kungiyar ASUU ake yin su kai tsaye.

Yawancin gine-ginen da ake da su a Jami’o’in Jiha da kayan aiki da kuma tallafin gudanar da bincike da horar da ma’aikata da habaka ayyukan su, ana samar kudaden ne ko dai ta asusun TETFUnd ko Kuma asusun NEEDs Intervention. Idan aka za a cire ayyukan TETFund da NEEDs daga Jami’o’in Jiha, to zasu koma kamar manyan makarantun sakandare ne. Don haka, ra’ayin cewa Jami’o’in Jihohi na yajin aikin hadin gwiwa kwata-kwata kuskure ne, rashin sanin ya kamata ne. Jama’a ya kamata su san cewa ASUU kungiya ce daya da ba za a iya raba su ba, kuma babu wani abu mai kama da Kungiyar ASUU ta Tarayya ko ta Jiha.

“Abin takaici ne yadda ASUU a wannan karon ke fama da Gwamnatin Tarayya marar tabbas da rashin gaskiya wadda ke ikirarin yaki da cin hanci da rashawa amma kuma ke tattare da gurbatattun abubuwa wadanda babban abin da ya damesu shi ne hana ‘yan kasa ingantacciyar rayuwa da ingantaccen ilimi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here