Ministan lafiya, Dakata Osagie Ehanire, ya ce akwai wadatattun likitoci a Najeria kuma gwamnatin tarayya zatai gaggawar mayar da gurbin duk wanda yabar aiki domin tafiya kasar waje aiki.
Ministan ya fadi hakan ne ranar Talata a Abuja ya yin taron manema labarai da ya hada.
Ya ce ba wani abinda ake boye ya yin daukar likitoci da kuma sauran ma’akatan lafiya a fadin kasa baki daya, abu ne wanda yake a bode.
“Mun karbe korafe-korafe kan barin aiki da jami’an lafiya sukeyi zuwa kasashen waje domin yin aiki a cen, amma maganar gaskiya ita ce bamu da matsala da tafiyar da suke yi, saboda muna da wadatattun likitoci, don duk shekara muna daukar jami’an lafiya 2,000 zuwa 3,000, sanan kuma adadadin likitocin da suke tafiya basu wuce mutum 1,000.”
“sai dai kawai akwai dokoki da ka’idoje wajan daukar ma’akatan” Inji shi.
Ya yin da yake magana kan batun yajin aikin da likitoci zasu tafi, ya ce suna iya kokarin su don ganin bata kai ga yajin aiki ba.
NAN














































