Shugaban hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta Najeriya NCDC ya shaida wa BBC cewa ɓarkewar cutar ‘murar mashaƙo’ ko ‘makarau’ a wasu sassan ƙasar a ‘yan kwanakin nan, ba abu ne da zai ɗaga wa ‘yan ƙasar hankula ba.
Kalaman na Dakta Ifedayo Adetifa na zuwa ne bayan da aka samu rahotonnin mutuwar mutum 25 a jihar Kano da ke arewacin ƙasar sakamakon kamuwa da cutar ta ‘murar mashako’ ko ‘maƙarau’, yayin da aka samu rahotonnin mutum 33 da suka kamu da cutar a wasu sasan ƙasar ciki har da birnin Legas.
Daga cikin alamomin cutar sun haɗar da zazzaɓi, da bushewar maƙogoro da tari da wahalar numfashi.
Waɗanda suka kamu da cutar kan fuskanci zafi a moƙogoronsu a lokacin haɗiyar miyau, da rikiɗewar idanu zuwa launin ja da launin ruwan toka a jikin kakin da suke tofarwa.
NCDC ta ce tana lura da mutanen da ake tsammanin sun kamu tare da bayar da shawara ga jama’a da su tabbatar da cewa sun karɓi allurar riga-kafin cutar musamman ƙananan yara.
Ana ɗaukar cutar ta hanyar tari da haɗa numfashi da mai ɗauke da ita, ko ta hanyar amfani da wasu abubuwa da mai ɗauke da cutar ya yi amfani da su kamar kofunan shan ruwa ko cokulan cin abinci da tufafi ko kwanciya waje ɗaya da mai ɗauke da cutar.
Dakta Adetifa ya ce bai kamata’yan kasar su ɗaga hankalinsu game da ɓarkewar cutar ba, saboda akwai wadatattun magunguna da riga-kafin da za su magance cutar.















































