Ranar Zazzabin Cizon Sauro ta Duniya : Gwamnatin Kano za ta yi wa yara miliyan 3 rigakafin Malaria

Kano Map
Kano Map

Gwamnatin jihar Kano na shirin yiwa yara miliyan uku da dubu ɗari da casa’in da uku da da biyu, tsakanin watanni 0 zuwa 59 don rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro a watan Yulin bana, in ji kwamishinan lafiya Dr Aminu Tsanyawa.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yau Litinin a wani taron manema labarai na tunawa da ranar zazzaɓin cizon sauro ta duniya na shekarar wadda ake gudanarwa duk shekara a ranar 25 ga watan Afrilu a fadin duniya domin wayar da kan jama’a game da annobar da ke ci gaba da laƙume rayuka tare da yin sanadiyyar yin tururuwar miliyoyin mutane zuwa asibiti.

Rana ce da ɗaukacin kasashe mambobin hukumar lafiya ta duniya WHO suka ware domin jaddada ƙarfin haɗin gwiwa da kuma alkawurran yaƙar cutar zazzabin cizon sauro da ake yi na tare da haɗa kai wajen cimma manufa ɗaya ta duniya da ba ta da zazzabin cizon sauro.

Taken bikin na duniya na bana shi ne “Kawo sababbin hanyoyi da dabaru don rage matsalar cutar Malaria da ceton Rayuka.”

Haka zalika taken na tare da yin kira na saka hannun jari da kirkire-kirkire da za su kawo sabbin hanyoyin shawo kan cutar zazzabin cizon sauro, bincike sake gano magungunan zazzabin cizon sauro da sauran kayayyakin aiki don hanzarta ci gaban da ake samu wajen yaƙi da cutar wadda ke da matuƙar tasiri da alamominta suka haɗa da zazzabi, sanyi, gajiya, rashin lafiya da rawar jiki, da gumi da amai da ciwon kai.

Tsanyawa, wanda Dr Ashiru Rajab, Daraktan kiwon lafiyar al’umma a ma’aikatar ya wakilta, ya ce “dukkan yaran da aka zayyana dole ne su kammala allurai hudu na rigakafi.”

Har ila yau, akwai matakin daƙile cutar ta hanyar yin alluran magungunan zazzabin cizon sauro kowane wata ga yara a lokacin yaduwar cutar.
Yin hakan yana da matuƙar tasiri don daƙile yaɗuwar zazzaɓin cizon sauro a tsakanin mutanen da ke da rauni ga tasirin cutar.
A cewarsa, ana buƙatar shan maganin gaba-ɗaya don yin tasiri mai sosai; don haka kada a taɓa yin amfani da shi bisa tsari.
Don haka kwamishinan ya buƙaci iyaye da su tabbatar da cewa ƴaƴansu sun samu tsawan kwanaki hudu na raba maganin rigakafin zazzabin cizon sauro.

Ya kuma yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu da su bayar da tasu gudunmawar da kuma tallafa wa gwamnati domin daƙile cutar ta Malaria.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here