Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da sabon ginin Cibiyar Yaki da Dakile Yaduwar Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) domin karfafa gwiwar jihar wajen ganowa tare da dakile bazuwar cututtuka masu yaduwa.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa Gwamnan ya kaddamar da cibiyar ne a ranar Litinin, wanda ke cikin Asibitin Kula da Cututtuka Masu Yaduwa (IDH) da ke Kano.
Ya bayyana cewa an kafa cibiyar ne domin daidaita ayyukan yaki da yaduwar cututtuka kamar su tarinfuka, AIDS/HIV, sankarau da sauran cututtuka masu yaduwa.
Gwamnan ya bukaci jami’an lafiya da su tabbatar da anyi amfani da cibiyar ta hanyar da ta dace domin amfanin al’ummar jihar.
“Ina kaddamar da wannan babban aikin lafiya, wanda wannan gwamnati ta tsara kuma ta aiwatar da shi. Wannan cibiya, wacce aka sanya wa suna Cibiyar Yaki da Dakile Yaduwar Cututtuka ta Jihar Kano, an samar da ita ne domin shawo kan duk wata cuta mai yaduwa kamar kanjamau, tarinfuka, sankarau, da sauran su.”
Ya nuna godiyarsa ga abokan habaka rukunoni da kuma jami’an Ma’aikatar Lafiya saboda gudunmawar da suka bayar wajen kafa cibiyar.
Tun da farko, Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa gwamnan ya cika alkawarin da ya dauka na kafa cibiyar yaki da cututtuka a jihar.
Labaran Yusuf ya jaddada muhimmancin cibiyar wajen inganta yaki da yaduwar cututtuka a jihar.
Ya kara da cewa abokan habaka rukunoni kamar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), African Field Epidemiology Network (AFENET), FMH 360, Core Group, FCDO, Lafiya, eHealth Africa da sauran su sun taka rawar gani kwarai da gaske wajen ganin an kafa wannan cibiya. (NAN)
















































