Kimanin mutum takwas ne aka tabbatar sun mutu sakamakon fashewar wata tankar dakon mai a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Lamarin ya ƙazance ne yayin da wuta ta kama a daidai lokacin da mazauna garin ke diban mai daga tankar da ta yi hatsarin a daren ranar Lahadi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta ce motar dakon man ta faɗi ne a kan titi, inda kusan dukkanin abubuwan da ke cikinta ya malale. Bayan haka ne mazauna yankin suka mamaye wurin domin dibar man.
“Motar tankar ta fashe inda ta kashe mutum takwas, ta kuma raunata wasu da dama wadanda aka garzaya da su asibiti, kamar yadda kakakin ‘yan sandan ya shaida wa BBC.
Mazauna yankin da shaidun gani da ido sun ce tankar ta fashe ne a wata unguwa da ke kusa da gidan mai, da kuma wani ginin coci amma babu ko daya da gobarar ta shafa.
Najeriya dai na fuskantar karin kusan kashi 400 na farashin man fetur tun watan Yuni bayan cire tallafin man da shugaba Bola Tinubu ya yi, matakin da ya ƙara iza wutar tsadar rayuwa da tsadar kayan masarufi.
Ƙasar wadda ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziƙi a Afirka tana shigo da sama da kashi 90 cikin 100 na man da take bukata saboda gaza tace danyen mai a cikin gida saboda lalacewar matatun mai mallakin gwamnati.