Majalisar alkalai ta kasa ta amince da nadin alkalai 63 na jihohi 16, 9 daga cikinsu shugabannin kotuna ne.
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na NJC, Soji Oye, ya sanyawa hannu a ranar Alhamis, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Majalisar ta kuma sanar da cewa wasu daga cikin manyan alkalai sun yi ritaya, wanda suka hada da mai shari’a Mudashiru Oniyangi na kotun daukaka kara, Bello Duwale na babbar kotun jihar Sokoto, SA Omonua da OS Uwuigbe na babbar kotun jihar Edo, MA Pindiga da Beatrice L. Iliya na babbar kotun. jihar Gombe.
Sauran sun hada da mai shari’a Kadi Muhammad O. Abdulkadir, Grand Kadi, kotun daukaka kara ta shari’a ta jihar Kwara da S. M. C. Ururuka-Ogeshi, shugaban kotun daukaka kara na gargajiya ta jihar Abia.
Haka kuma ta samu sanarwar rasuwar alkalai A. K. Fowe, babban kotun jihar Ekiti, Chinonyerem Onii, babbar kotun jihar Imo da Kadi Shehu Ibrahim Ahmad, Grand Kadi, jihar Kaduna.
Sanarwar ta kara da cewa, haka ma majalisar ta amince da karin girma ga ma’aikata 84 daga matakin albashi na mataki na 7 zuwa 17 kamar yadda kwamitin nada, karin girma da kuma ladabtarwa ya gabatar.













































