Alhaji Hashimu-Shehu Gazura, kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta Zamfara (ZASIEC), ya rasu.
Ya rasu ne a wani mummunan hatsari a ranar Juma’a.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa Gazura kuma tsohon dan majalisar dokokin jihar Zamfara ne, mai wakiltar mazabar Gummi 2 .
Rasuwar tasa na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Shugaban Hukumar Majalisar dokokin jihar, Alhaji Mansur Bungudu ya fitar a Gusau ranar Asabar.
“Ya rasu ne a jiya (Juma’a) sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a hanyar Yawuri a jihar Kebbi. Inji sanarwar.
“An shirya yin sallar jana’izar marigayin a fadar Sarkin Gummi ranar Asabar da karfe 11:00 na safe.













































