Karamar hukumar Madobi ta samar da filin sallar idi ga al’ummar MARAYA-BURJI.

IMG 20221105 WA0003
IMG 20221105 WA0003

Daga:Aminu Bala Madobi.

Karamar hukumar Madobi ta kaddamar da mika katafaren fili ga al’ummar MARAYA-BURJI Dan cigaba da aiwatar da ibadar dakuma sallar IDI.

Shugaban karamar hukumar Madobi,Alh. Muhammad Lawan Yahaya ya bayyana haka lokacin gangamin mika babban filin ga al’ummar yankin tareda dashen daruruwan bishiyoyi da yasami halartar masu ruwa da tsaki da manyan mukarraban gwamnati.

Muhammad Lawan Yahaya yace hakan na zuwa ne bayan kiraye-kiraye da alummar Garin sukayi na bukatar samar musu babban filin gudanar da ibadar sallar idin.

Shugaban karamar hukumar wanda ya sami wakilcin shugaban Ma’aikata Alh Auwal Sanusi Gora yace shugabancin karamar hukumar za ta cigaba da bujuro da ayyukan cigaba na more rayuwa ga kafatanin mazabun yankin 12 a kokarin jibantar lamuran jama’ar da akewa jagoranci.

Alh Auwal Gora daganan yace sunabin kowanne matakan ayyukan raya kasa daki-daki, kana yace karamar hukumar tayi nisa wajan inganta kiwon lafiya, makarantu, gyaran hanyoyi, famfunan tuka-tuka da inganta rayuwar mata da matasa dake lungu da sakunan karamar hukumar.

Shugaban Ma’aikatan daganan ya bukaci alummar yankin dasu bada tasu gudun-mawar wajen baiwa bishiyun da aka dasa ruwa la’akari da gabatowar lokacin rani dan samun cin gajiyar su.

A tsokacin dayayi me unguwar MARAYA-BURJI ya godewa shugabancin karamar hukumar bisa namijin kokarin sama musu irin wannan fili na gudanar da sallar idin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here