Alkalin Alkalan Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta rantsar da Sagir Suleiman Gezawa, Mas’ud Mobolaji Alabelewe da wasu lauyoyi 66 a matsayin Manyan Lauyoyin Najeriya (SAN), yayin buɗe bikin shekarar shari’a ta 2026/2027.
Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA) ne ya sanar da hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, inda ya wallafa hotuna da bidiyo daga bikin rantsarwar.
Read also: UNILAG Ta Rage Kudin Makaranta, Bayan Taron Da Kungiyar Dalibai Ta Kasa Tayi Da Shugaban Jami’ar
Rantsarwar ta biyo bayan amincewa da sunayen mutane 68 da Kwamitin Bai Wa Lauyoyi Matsayin Manyan Lauyoyin Kasa (LPPC) ya yi kusan watanni uku da suka gabata.
Kwamitin ya amince da ɗaukaka matsayin waɗannan lauyoyi ne a yayin zamansa na 174, wanda Kekere-Ekun ta jagoranta.
A cewar wata sanarwa da Babban Rijistaran Kotun Ƙoli ta Kasa da kuma malamin jami’a guda ɗaya.
SolaceBase ta rawaito cewa Sagir Suleiman Gezawa shi ne babban jagoran kamfanin lauyoyi na S.S. Gezawa and Co., inda ya shafe sama da shekaru 20 yana aikin lauya.
Read also: An nada wa Jami’ar Sule Lamido ta Jihar Jigawa sabon shugaba
Shi mamba ne mai daraja ta musamman a Cibiyar Masu Sasanta Rikice-rikice ta Chartered Institute of Arbitrators da ke Birtaniya.
Ya taɓa zama Babban Lauyan Ba da Shawara a kamfanin K. T. Turaki & Co., sannan ya riƙe matsayin Manajan Abokin Hulɗa a kamfanin Century Attorney. A halin yanzu, shi ne babban abokin hulɗa na kamfanin S.S. Gezawa and Co.
Gezawa ya taɓa zama shugaban ƙungiyar lauyoyi ta kasa (NBA), reshen jihar Kano.
Matsayin Babban Lauyan Najeriya (SAN) na ɗaya daga cikin manyan karramawa da ake bai wa ƙwararrun lauyoyi a fannin shari’a a ƙasar.
Read also: ‘Yar Najeriya ta kammala girkin sa’a 120 don kafa tarihi a duniya
Ana bai wa lauyoyi wannan matsayi ne bisa cika ƙa’idojin ƙwarewa da nasarori a fannin kare haƙƙin abokan harka a kotu ko kuma fannin ilimin shari’a.













































