Rikicin da ya barke tsakanin kungiyar NLC da na LP ya sake daukar wani sabon salo, yayin da mambobin kungiyar ta NLC, a ranar Larabar da ta gabata suka karbi hedikwatar jam’iyyar da ke unguwar Utako a Abuja.
Mambobin kungiyar karkashin jagorancin mukaddashin shugaban kwamitin siyasa na majalisar, Theophilus Ndubuaku, sun bukaci Julius Abure da ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban jam’iyyar na kasa nan take saboda ba a zabe shi a matsayin shugaban jam’iyyar Labour ta kasa ba.
Karin labari: Para-Athletes: Sunyi zanga-zangar biyan su alawus da neman aiki
Shugaban hukumar siyasar NLC ya kuma yi ikirarin cewa taron da jam’iyyar ta shirya yi a karkashin jagorancin Abure haramun ne.
Babban taron da aka ce zai gudana a Umuahia babban birnin jihar Abia a ranar 27 ga watan Maris, kungiyar NLC ta yi zargin cewa da nufin sake zaben Abure a matsayin shugaban jam’iyyar Labour kadai, tare da fargabar sirrin da ke tattare da hakan.
Kungiyar NLC dai na neman a kafa kwamitin rikon kwarya domin shirya taron kasa na jam’iyyar da ya dace da kuma bai daya.
Karin labari: An kashe jami’ai 15 a wani harin kwantan ɓauna a Sudan ta Kudu
Duk da cewa babu wani jami’in jam’iyyar a hedikwatar, amma shugabannin kwadago sun mamaye harabar jam’iyyar yayin da jami’ai da jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya suka sanya ido a sakatariyar domin gujewa barna.
‘Yan kungiyar da suka ci gaba da zama a hedikwatar jam’iyyar Labour, suna rera wakokin adawa ga Abure, suna zargin shugaban jam’iyyar da wawure kudade.
Sai dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta hana ma’aikatan da suka yi zanga-zangar shiga sakatariyar jam’iyyar.