An kashe mata biyu a cibiyar addinin musulunci a Lisbon

1680019918947
1680019918947

‘Yan sanda sun ce wani mahari ya kashe wasu mata biyu, bayan da ya daɓa musu wuƙa a wata cibiyar addinin musuluci a birnin Lisbon na ƙasar Portugal.

An kai harin ne a cibiyar addinin musulunci ta ‘Ismaili Centre’ da ke birnin

‘Yan sanda sun samu nasarar harbe maharin – wanda ke riƙe da sharɓeɓiyar wuƙa – a ƙafa, bayan da ya yi yunƙurin guduwa.

Kawoyanzu dai ba a san dalilin maharin na kashe matan ba.

‘Yan sanda sun ce sun samu kiran waye inda aka shaida musu cewa an ga maharin ya shiga cibiyar da misalin ƙarfe 11 na safe agogon ƙasar.

Shugaban cibiyar Nazim Ahmad ya ce maharin ɗan Afghanista ne, yayin su kuma matan biyu ‘yan Portugal ne.

A wata sanarwar da cibiyar addinin ta fitar a shafinta na intanet ta ce ta kaɗu matuƙa da kisan matan, tare da alƙawarta bayar da tallafi ga iyalan mamatan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here