China ta ki amincewa da bukatar gwamnatin Buhari ta ranto sama da tiriliyan 10

IMG 20230329 WA0000
IMG 20230329 WA0000

Bankin China-Exim ya ki amincewa da bukatar lamunin Gwamnatin Najeriya na ranto zambar nera tiriliyan N10.12trn daidai da Dalar amurka $22,798,446,773.

Rahotanni sun nuna cewa an yi watsi da lamunin da aka ki amincewa da shi ne don tallafawa aikin sabunta layin dogo na Najeriya na sashin Kaduna-Kano.

Rahotannin sun ce irin badakalar da akayi yasanya China ta nuna damuwa game da ikon Najeriya na biyan bashin da kuma tasirin rabon tallafin cutar COVID-19 a cikin aikin, bankin Exim na China ya janye tallafinsa.

A halin da ake ciki, Majalisar Wakilai, a zamanta na ranar Talata, 28 ga Maris, 2023, ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na karbar bashin dala miliyan 973,474,971.38 daga bankin raya kasar Sin.

Shugaban Kwamitin Dokoki da Kasuwanci na Majalisar, Abubakar Fulata, ya gabatar da kudiri ga majalisar dokokin da ta yi gyara ga kudurin da ta amince da yarjejeniyar rancen da ta gaza.

Da yake gabatar da kudirin, Fulata ya ce, “Majalissar ta lura da cewa, shirin 2016-2018 na Gwamnatin Tarayya na karbar bashi ya samu amincewar Majalisar Dattawa da ta Wakilai a ranar 5 ga Maris, 2020, da 2 ga Yuni, 2020, bi da bi.

Don haka Fulata ya roki majalisar da ta janye hukuncin da ta yanke kan masu kudi tare da daidaita sharuddan, sannan ta amince da sauyawa daga bankin Exim na kasar Sin zuwa bankin raya kasar Sin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here