Hukumar NDLEA ta kama wasu mata biyu masu ciki suna shirin safarar miyagun kwayoyi a Lagos

NDLEA
NDLEA

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce ta kama wasu mata biyu masu ciki a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Lagos suna shirin safarar miyagun kwayoyi.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce tun a ranar laraba, 4 ga watan Mayun 2022 ta kama wasu katan-katan din kwayoyi da kwalaben giya, inda nan take aka kama wadda ta kai kayan don aikawa da su Dubai mai suna Shola Ogunrinde.

Binciken da hukumar ta gudanar ne ya sa aka kama wata mace mai ciki mai suna Seun Babatunde, waddda ke gudanar da harkokin sayar da kayan maye a Iyana da ke Lagos.

Jami’in yada labaran hukumar, Femi Babafemi, ya ce an kama mai ciki ta biyun ne mai suna Gloria Asibor, lokacin da take kokarin shiga jirgi zuwa kasar Spaniya dauke da kwayar Tramadol 300 mai nauyin kilo giram 200 da kuma 225.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here