A ranar litinin din nan ne jam’iyyar PDP zata gudanar da taron ta na shiyyar Arewa-maso-Yamma domin zabar shugabanni da kuma dattawan jam’iyyar na kasa a shiyyar.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar ranar Asabar a birnin Abuja.
Sakataaren yada labaran yace Kwamitin kolin Jam’iyyar na kasa, ya amince da gudanar da taron a shelkwatar jam’iyyar da ke Jihar Kaduna.
Haka zalika kwamitin ya bukaci dukkan shugabanni, da masu ruwa da tsaki a yankin Arewa-maso -Yamma da su bi ka’idoji domin yin zabukan cikin kwanciyar hankali ba tare da wani hargitsi ba.













































