Gwamna Yusuf ya sauke Kwamishina daga muƙaminsa

Abba Kabir Yusuf Kano Kano 715x430

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sauke Alhaji Shehu Wada Sagagi daga muƙaminsa na Kwamishinan harkokin kasuwanci masana’antu da jam’iyyun gama Kai da kuma zuba jari.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da tsakar daren wayewar yau Alhamis 26 ga watan Maris ce ta bayyana hakan.

Sanarwar ta ce, gwamnan, ya umarci tsohon kwamishinan da ya mika ragamar ma’aikatar ga Daraktan harkokin kasuwanci nan ta ke.

Haka kuma, gwamna Abba Kabir Yusuf, ya gode masa bisa ayyukan da ya yi a lokacin da ya ke kan mukamin.

Gwamnan ya yaba da gudunmawar Sagagi wajen ci gaban jihar Kano musamman ma a fannoni na siyasa, addini da bunƙasa kanana da matsakaitan sana’o’i.

Ya kuma yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da inganta ayyukan jama’a da shugabanci nagari, inda sanarwar ta ce an yi sauyin ne domin ƙara inganta ayyukan gwamnati.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here