Gwamnatin jihar Kano ta sanar da nasarar ceto sakataren gudanarwa na karamar hukumar Kibiya, Alhaji Hamza Durya, bayan da aka sace shi.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an sace Durya ne a karshen mako a gidansa da ke kauyen Durya a karamar hukumar Kibiya, lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka dauki matakin gaggawa a fadin jihar.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa jami’an Hukumar tsaron farin kaya ta DSS reshen jihar Kano sun gudanar da wani aiki cikin gaggawa da hadin gwiwa wanda ya kai ga ceto mutumin lafiya.
Sanarwar ta ce an kama mutane biyu da ake zargi da satar mutane a yayin aikin, inda aka bayyana cewa sun samu raunukan harbin bindiga.
Gwamnatin ta bayyana wannan nasara a matsayin babban ci gaba, tana mai cewa hakan na nuna jajircewa da kwarewar hukumomin tsaro da ke aiki a jihar.
Ta yabawa DSS da sauran jami’an tsaro kan saurin daukar mataki da kuma sadaukarwarsu wajen kare rayuka da dukiyoyi, tana mai cewa wannan nasara na nuna ingancin dabarun tsaro da ake aiwatarwa a dukkan kananan hukumomi 44 na jihar.
Sanarwar ta kuma yaba da rawar da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ke takawa wajen tallafawa hukumomin tsaro da samar musu da kayan aiki, wanda hakan ke kara inganta aikinsu.
Gwamnatin ta tabbatar wa al’umma cewa za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro, tare da kira ga jama’a da su kasance masu lura da kuma sanar da hukumomin tsaro duk wani abu da ya dauki hankalinsu, domin tabbatar da cewa jihar Kano ta ci gaba da kasancewa mai zaman lafiya ga kowa.