Tun bayan da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar da mataimakin gwamnan Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin magajin gwamnan, kwatsam sai daya daga cikin masu neman kujerar, Inuwa Ibrahim Waya, ya sake jaddada kudirin sa na neman gwamnan, inda ya nemi ayi zaben fidda gwani.
Wata majiya mai tushe daga tsagin daya daga cikin masu neman kujerar, Barista Ibrahim Inuwa Waya, ta shaidawa Jaridar NIGERIAN TRACKER, cewa shi a shirye yake daya tsaya takara a zaben fidda gwani, tsakanin sa da mataimakin gwamna, wanda za a gudanar a ranar 17 ga watan Mayu, domin ya gwada sa’ar sa.
Ibrahim Inuwa Waya dai ya fito ya tsunduma cikin harkokin siyasa ne bayan da ya ajiye aikin sa a Kamfanin tarraba man fetur na kasa wato NNPC.













































