ICPC ta kai samame gidan El-Rufai

Nasir El Rufai

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta kai samame gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Abuja a ranar Alhamis.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya wallafa a shafinsa na X a daren Alhamis, ya ce jami’an hukumar yaƙi da rashawar sun binciki gidan.

Ya ce lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya yi tir da matakin, yana mai cewa ya saɓa wa doka kuma ya keta ƙa’idojin shari’a da haƙƙoƙin ɗan adam.

A daren Laraba, ICPC ta sanar da cewa ta tsare tsohon gwamnan dangane da bincike da ake yi.

Kafin tsare shi da ICPC ta ui, hukumar EFCC ta riƙe shi tun ranar Litinin bayan ya amsa gayyatar da ta aika masa a hedikwatarta.

Majiyoyi sun ce an yi masa tambayoyi a hedikwatar EFCC kan zargin almundahanar kuɗaɗe a lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.

A shekarar 2024, Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta tuhume shi da karkatar da Naira Biliyan 423 na kuɗaɗen jama’a da kuma wankiyar kuɗi, tare da neman hukumomin yaƙi da rashawa su bincike shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here