Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya rusa Majalisar Zartarwar Jihar tare da sallamar dukkan masu ba shi shawara na musamman.
Fubara ya kuma nada sabon Babban Sakataren Yada Labarai, Mista Onwuka Nzeshi.
Tsohon sakataren yaɗa labaran sa, Nelson Chukwudi, shi ma an sauke shi daga mukaminsa.
Sai dai ba a bayyana dalilin sauke Chukwudi ba.
Bayanin rushewm majalisar na cikin wata Sanarwa ta Musamman da gwamnatin jihar ta fitar a Fatakwal ranar Alhamis, wadda Nzeshi ya rattaba hannu a kai.
Fubara ya umarci kwamishinoni da masu ba shi shawara na musamman da su mika ragamar ofisoshinsu ga manyan Sakatarori ko manyan jami’an ma’aikatunsu nan take.
Gwamnan ya kumkuma nuna matukar godiyarsa ga mambobin majalisar da suka sauka, tare da yi musu fatan alheri a kokarinsu na gaba.
Sabon matakin na iya alaka da yarjejeniyar sulhu da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta tsakanin Fubara da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a Abuja.
Wannan ne karo na uku da Tinubu ke shiga tsakani a rikicin siyasar Rivers tsakanin gwamnan da tsohon jagoransa na siyasa da kuma ‘yan majalisar dokokin jihar.
Da wannan mataki, ana sa ran Fubara zai mika sabon jerin sunayen wadanda zai nada kwamishinoni ga Majalisar Dokokin Jihar karkashin jagorancin Martin Amaewhule domin tantancewa da amincewa.
Rahotanni sun nuna cewa a cikin yarjejeniyar da aka cimma da Wike, Fubara zai karbi wasu daga cikin magoya bayan tsohon gwamnan cikin sabuwar majalisar zartarwarsa, yayin da wasu daga cikin kwamishinonin da suka yi aiki da shi da aka sallama na iya komawa.













































