Hukumar kula da gidajen yari da kungiyar Lauyoyi masu bada agaji sun tabbatar da sakin fursunan Kano bayan shafe shekaru 22 a tsare

Kano Ccentral Prison

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa (NCoS), reshen Jihar Kano, tare da hadin gwiwar kungiyar Bayar da Agajin Lauyoyi ta kasa (Legal Aid Council of Nigeria), sun tabbatar da sakin wani fursuna da ya shafe shekaru 22 a tsare kan zargin fashi da makami.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar NCoS a Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce tun farko wata Babbar Kotun Shari’a ta yanke masa hukuncin yanke hannunsa na dama da kafarsa ta hagu.

Rahotanni sun nuna cewa fursunan, wanda dan kasuwa ne a kasuwar titin Galadima da ke Sabon Gari, an zarge shi da azabtarwa a hannun rundunar yaki da fashi da makami ya musamman (SARS), inda aka karya masa hannayensa biyu, aka karbe masa Naira 800,000 tare da babur dinsa, sannan aka tilasta masa amsa laifin da bai aikata ba.

Sanarwar ta ce, bayan ci gaba da kokarin shari’a da daukaka kara da Barr. Asiya Mohammed-Imam ta kungiyar Legal Aid Council a Kano ta jagoranta, kotu ta sake duba shari’ar tare da wanke shi daga zargi sannan ta sallame shi.

Ta kara da cewa wannan mataki na nuna kokarin da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ke yi na rage cunkoso a gidajen ajiya tare da tabbatar da cewa fursunoni na samun adalci da wakilcin shari’a yadda ya kamata.

A cewar sanarwar, hadin gwiwar da ke tsakanin NCoS da hukumar ya nuna aniyar bangarorin biyu na bin ka’idojin doka, daidaito da kuma kare hakkokin fursunoni.

Ta ce yayin da yake tsare, fursunan ya shiga shirye-shiryen ilimi da koyon sana’o’i domin tallafa wa gyaran halinsa da saukaka komawarsa cikin al’umma.

Bayan sakinsa, ya nuna godiya ga hukumar kan shirye-shiryen gyaran hali da kuma inganta jin dadin fursunoni.

Hukumar ta kuma jaddada kudirinta na tabbatar da adalci, tsarewa cikin mutuntaka, gyaran hali da kuma sake shigar da fursunoni cikin al’umma bisa ka’idojin duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here