Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya zargi shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki da ruguza ‘yan adawa.
Tambuwal yayi wannan zargi a ranar Juma’a lokacin da aka nuna shi a gidan Talabijin na Channels a shirin Siyasa a yau, yana mai ikirarin cewa da gangan APC da Tinubu suka shirya faduwar jam’iyyun adawa a kasar.
“Idan ka kalli abin da ke faruwa a jam’iyyun siyasa daban-daban a Najeriya a yau – ba ka bukatar a gaya maka, ko da kuwa yawan musun da kowa ya yi, ciki har da shugaban kasa Bola Tinubu, cewa ba su da hannu a yunkurin tada zaune tsaye na jam’iyyun adawa,” in ji Tambuwal a kan al’amuran yau da kullum.
“Ba wai ina zarginsu bane, ina cewa suna da hannu a yunkurin da ake yi na kawo cikas ga jam’iyyun adawa,” in ji shi












































