Duk da musun da gwamnatin Edo ta yi, wata takarda ta umarci malamai a jihar su cire Ciyawa a makarantu

Monday Okpebholo 750x430

Wata takarda daga Hukumar kula da manyan makarantun Sakandare ta umarci malamai su share ciyawa da tsaftace makarantunsu kafin fara sabon zangon karatu

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya ruwaito cewa wannan umarni ya sabawa maganar farko ta gwamnatin jihar, wadda ta ce ba ta tilasta wa malamai yin ayyukan da suka shafi share-share ba.

Takardar, wadda aka sanya wa hannu a ranar 27 ga watan Agusta ta hannun Obarisiagbon M. I. a madadin shugabar hukumar, Dr. Maureen Ekhorangbon, an tura ta ga dukkan shugabannin makarantu. An bayyana ‘cewa tsaftace muhalli zai tabbatar da tsabta, kariya, da kuma koya wa ɗalibai da’a da aikin sa kai.

Takardar ta umurci malamai su fara aikin daga 1 ga Satumba, sannan ɗalibai su dawo makaranta a ranar 8 ga Satumba. An kuma umurci shugabannin makarantu su jagoranci aikin kai tsaye, sannan su tura hoton shaida na abin da aka yi zuwa ga hukumar ta WhatsApp kafin 5 ga Satumba.

Karanta: Tinubu ya naɗa Bunkure a matsayin shugaban Jami’ar Tarayya ta Zariya, ya naɗa Nakore da Kodage a majalisar gudanar a Jami’ar ilimi ta tarayya a Kano

Takardar ta ƙara jaddada cewa aikin wajibi ne ga kowa, kuma wani ɓangare ne na ci gaba da aiwatar da shirin gyaran ilimi na gwamnan jihar.

Sai dai, wannan ya tabbatar da damuwar kungiyoyin farar hula da ke cewa ana tilasta wa malamai aikin share makarantu. Duk da haka, ma’aikatar ilimi ta jihar ta musanta wannan batu a wata sanarwa, inda ta ce ba gaskiya ba ne, domin duk wani aikin tsaftacewa daga malamai aikin sa kai ne kawai (CSR).

NAN ta ruwaito cewa makarantun jihar Edo za su koma ne a ranar Litinin domin fara zangon karatu na shekarar 2025/2026.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here