An gyara babban layin wutar lantarki, yayin da harkokin samar da wuta ya koma daidai – NISO

Power Power (1)

Hukumar sarrafa tsarin wutar lantarki mai zaman kanta ta Nijeriya ta tabbatar da cewa an dawo da tsarin wutar lantarki na ƙasa gaba ɗaya, inda samar da wutar lantarki ya koma daidai a dukkan yankunan da matsalar ta shafa.

Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da shugabancinta ya fitar a birnin tarayya Abuja a ranar Talata, yayin da take bayar da ƙarin bayani kan tangardar da ta samu a wani ɓangare na tsarin wutar lantarki na ƙasa.

Sanarwar ta nuna cewa da misalin ƙarfe 10:48 na safe, an samu matsalar tashin wutar lantarki a tsarin wutar lantarki na ƙasa, wadda ta samo asali daga tashar wutar lantarki ta Gombe.

Matsalar ta bazu cikin gaggawa a fadin tsarin wutar lantarki, inda ta shafi tashoshin wutar lantarki na Jebba da Kainji, sannan daga bisani tashar wutar lantarki ta Ayede.

Lamarin ya haifar da katsewar wasu layukan wutar lantarki da kuma na’urorin samar da wuta, wanda ya janyo tangardar tsarin wutar lantarki a wani ɓangare na ƙasar, amma ba cikakken rushewar tsarin ba.

Hukumar ta nuna cewa an ɗauki matakan gaggawa nan take domin daidaita tsarin tare da dawo da ayyukan wutar lantarki yadda ya kamata, inda aikin dawo da wutar ta fara da misalin ƙarfe 11: 11 na safe.

NAN

.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here