Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin shugabannin kwamitoci da manyan daraktoci a hukumomi 42 na tarayya, tare da sakataren Hukumar Kare Farar Hula, Shige da Fice, da Gidajen Yari.
A cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa nadin ya fara aiki nan take.
Daga cikin wadanda aka nada sun hada da Abdullahi Ganduje a matsayin Shugaban Hukumar Filayen Jiragen Sama (FAAN), Nasiru Gawuna a matsayin Shugaban Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya, da Tokunbo Afikuyomi a Hukumar Kula da Fasaha (NOTAP).
Ga wasu daga cikin sunayen:
Ganduje: Shugaban FAAN
Gawuna: Shugaban Federal Mortgage Bank
Tokunbo Afikuyomi: Shugaban NOTAP
Kayode Opeifa: MD na Nigerian Railway Corporation
Magnus Abe: Shugaban NA Great Green Wall
Shugaban ya gargadi shugabannin da kada su tsoma baki cikin ayyukan gudanarwa domin mukamansu ba na aiwatarwa ba ne.