Hukumar kula da gidajen waya ta Kasa NIPOST ta musanta korar Shugaban ta

Ismail Adebayo Adewusi 750x430 1
Ismail Adebayo Adewusi 750x430 1

Hukumar kula da gidajen waya ta kasa NIPOST ta karyata wani rahoto da ke ci gaba da yaduwa cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kori shugaban hukumar na tarayya Dakta Ismail Adebayo Adewusi.

Hukumar ta NIPOST a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, mai dauke da sa hannun Daraktan sashen yada labaran ta Franklyn Alao, ta ce labarin karya ne ba shi da makama.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An jawo hankalin hukumar ta NIPOST kan rahoton da ke ci gaba da yaduwa mai taken “Buhari Ya Kori shugaban hukumar NIPOST”

Sanarwar ta ce, har yanzu Dakta Ismail Adebayo Adewusi, shi ne shugaban Hukumar kuma yana ci gaba da gudanar da ayyukansa ba tare da gajiyawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here