Mai horas da kungiyar ‘yan wasan Najeriya ta Super Eagles, Jose Peserio yace a rayuwarsa bai taba hannu da wani shugaban kasa ba, sai wannan karo da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karrama shi a fadar sa da ke Abuja.
Peserio ya bayyana haka ne cikin farin ciki lokacin da Tinubu ya karrama tawagar ‘yan wasan da suka taka rawar gani a gasar AFCON da aka kammala a kasar Kwaddebuwa.
Karanta wannan: ‘Yan sanda sun kama mutum 400 da ake zargi da aikata laifuka a Legas
Kungiyar Super Eagles ta samu lambar azurfa saboda zuwa na 2 a gasar, bayan ta sha kashi a hannun ‘yan wasan Kwaddebuwa. wadanda suka lashe gasar.
Shugaba Tinubu ya jinjinawa tawagar Super Eagles wadda ta kun shi ‘yan wasan da masu horar da su, tare da basu lambar girma ta kasa da kuma gidaje kyauta a Abuja.
Karanta wannan: Kungiyar masu gidan burodi za su soma yajin aikin gama gari
Wannan karramawar ta yi matukar farantawa Peserio rai, wanda bai boye a zuciyarsa ba, inda ya jinjinawa gwamnatin Najeriyar da kuma shugaban kasa Bola Tinubu wanda ya karbe su.
A wurin ne Peserio yace a rayuwar sa bai taba hannu da wani shugaban kasa ba, sai a wannan karon.
‘Yan Najeriya da dama sun bayyana gamsuwa da rawar da kungiyar Super Eagles ta taka a gasar ta AFCON duk da rashin nasarar lashe kofin.