Shugaba Tinubu zai tashi zuwa kasar Ethiopia

Tinubu, kasar, Qatar, Najeriya, Legas, kasuwanci
A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu zai bar Najeriya zuwa kasar Qatar bisa gayyatar Sheikh Tamin Al-Thani sarkin Qatar. Kamar yadda Ajuri Ngelale, mai...

A ranar Alhamis ne shugaba Bola Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Ya ce Tinubu zai halarci zaman taron shugabannin kasashe da gwamnatocin Tarayyar Afirka AU karo na 37.

Karanta wannan: “Ban taba yin hannu da shugaban wata kasa ba” – Peserio

Taken taron shi ne ”Koyar da wani dan Afirka da ya dace da karni na 21: Gina tsarin ilimi mai juriya don kara samun dama ga ci gaban ilimi da tsawon rai da inganci da kuma dacewa da koyo a Afirka”.

Ngelale ya ce, shugaban zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afirka a manyan tarukan da suka shafi sauye-sauyen hukumomin kungiyar ta AU, da zaman lafiya da tsaro musamman batutuwan da suka shafi sauyin yanayi da kuma hanyoyin shiga da kuma abubuwan da suka sa a gaba a kungiyar ta G20.

Karanta wannan: Kotu ta daure Aisha Alkali Wakil kan laifin damfarar Naira Miliyan 40

A wajen taron mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Tinubu zai kuma halarci wani babban taro na musamman na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS a matsayinsa na shugaban kungiyar na yankin.

Ya ce shugaban wanda zai samu rakiyar ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati a wannan tafiya ana sa ran zai dawo Abuja a karshen taron.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here