Yanzu-Yanzu: Makinde ya jagoranci nada Turaki shugaban PDP na rikon kwarya na kasa

Turaki (1)

Jam’iyyar PDP tsagin da ke samun goyon bayan Gwamnan Jihar Oyo Seyi Makinde, ta nada Kabiru Tanimu Turaki (SAN) a matsayin Shugaban Kwamitin na Rikon Kwarya na Kasa.

An nada Turaki ya jagoranci tawagar rikon kwarya mai mambobi 13 a ranar Litinin yayin taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) karo na 103 da jam’iyyar ta gudanar a Abuja.

An yanke wannan shawarar ne bayan wani kuduri da Shugaban PDP na Jihar Edo, Tony Aziegbemi, ya gabatar kuma Clement Fagboyede, mamba na musamman, ya mara masa baya.

Bangaren da ke tare da Gwamna Makinde ta kuma amince da cikakken jerin sunayen shugabannin rikon kwaryar da aka dora wa alhakin tafiyar da harkokin jam’iyyar.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Taofeek Arapaja a matsayin Sakataren Kasa, tare da Daniel Ambrose, Hamza Abuya, Ihediwa, Isah Abubakar, Theophilus Dakashan, Ini Ememobong, Aribisala Adewale Idowu, Baru Shaffi, da Okechukwu Obiechina.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here