Jam’iyyar APC ta amince da karin wa’adin sayarwa da mika cikakkun fom din nuna sha’awa da tsayawa takara na masu neman takara, tare da tsarin tantancewa domin babban zaben shekarar 2027.
Jam’iyya mai mulki ta sanar da karin wa’adin a ranar Litinin a cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Felix Morka, ya sanya wa hannu.
A cewar sanarwar, an kara wa’adin sayar da fom har zuwa daren, Laraba, 6 ga Mayun shekarar 2026.
APC ta ce an kara wa’adin mika fom har zuwa daren, Alhamis, 7 ga Mayun shekarar 2026.
Ta kuma kara da cewa tantance masu neman takara yanzu za a yi shi daga Juma’a, 8 ga Mayun shekarar 2026 zuwa Talata 12 ga Mayun.
Sabuwar ranar fitar da sunayen wadanda aka tantance ita ce Laraba, 13 ga Mayu, 2026.
Karin wa’adin sayar da fom din tsayawa takara da APC ta yi domin zaben 2027 na zuwa ne saboda yawan bukatar masu neman takara.












































