Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar wa Gwamnan Ebonyi Umahi takarar sanata

FB IMG 16706824558513786
FB IMG 16706824558513786

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar wa Gwamnan Ebonyi Dave Umahi takararsa ta kujerar sanata da yake yi a babban zaɓen 2023 mai zuwa.

Cikin wani matakin bai-ɗaya da suka yanke, rukunin alƙali biyar na kotun ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Kudirat Ekekere-Ekun sun kori ƙarar da mai adawa da takarar tasa Princess Ann Agom-Eze ta shigar a ranar Juma’a.

Kafofin labarai a Najeriya sun ruwaito cewa alƙalan sun amince cewa ƙarar ba ta cancanci a saurare ta ba kuma dalilin da ya sa suka kore ta kenan.

Agom-Eze ta kai ƙarar ce da zimmar kotun ƙolin ta jingine hukunce-hukuncen da Babbar Kotun Tarayya da Kotun Ɗaukaka Ƙara suka yi na amincewa da sakamakon zaɓen da ya ayyana Umahi a matsayin wanda ya yi nasara.

Ita ce ta zo ta biyu a zaɓen da aka gudanar lokacin da aka bayyana Austin Umahi a matsayin wanda ya yi nasara, wanda ɗan uwa ne ga Gwamna Dave Umahi.

Sai dai gwamnan ya shiga takarar ce bayan kayen da ya sha a zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin ƙasa, inda ƙaninsa Austin ya janye tare da ba shi tikitin takarar.

Hakan na nufin wannan ne hukunci na ƙarshe da za a yi a shari’ar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here