Wike, Tinubu yake goyon baya ba APC ba – Oshiomhole

Adams Aliyu Oshiomhole
????????????????????????????????????

Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, Shugaban Kasa Tinubu yake goyon baya, ba jam’iyyar APC ba.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake amsa tambayoyi a wata hira da gidan talabijin na TVC.

Kalaman nasa sun biyo bayan takaddamar da ta kunno kai tsakanin Wike da wasu gwamnonin APC, bayan da ministan ya bayyana wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar a matsayin “marasa himma a siyasa.”

Tsohon gwamnan Jihar Edon ya bayyana cewa, duk da cewa Ministan Abuja ba ɗan jam’iyyar APC ba ne, ya sha bayyana goyon bayansa ga Shugaba Tinubu.

“Wike yana goyon bayan Shugaba Tinubu ne, amma ba APC ba. Matsayar wasu daga cikin gwamnonin APC da ta ministan ɗaya ce. Dukkansu sun himmatu wajen goyon bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu.

“Ni na gamsu da cewa ɓangarorin biyu suna aiki ne domin cimma manufa guda, wato goyon bayan Shugaban Ƙasa.

“Ban ji wani ɓangare na wannan muhawara yana nuna cewa wani, har da Ministan Abuja, yana adawa da sake zaɓen Shugaba Tinubu ba.

“Shi da kansa ya sha faɗa cewa shi ba ɗan APC ba ne, ba ya cikin APC, amma yana goyon bayan Shugaban Ƙasa,” in ji Oshiomhole.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here