Gwamnatin Tarayya ta ayyana Alhamis a matsayin ranar hutu

Minister of Interior Dr. Olubunmi Tunji Ojo

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 1 ga Oktoban 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, a cikin wata sanarwa da sakatariyar dindindin ta ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta sanya wa hannu a ranar Laraba.

Tunji Ojo ya taya al’ummar Najeriya na gida da waje murnar zagayowar ranar samun ’yancin kan kasar, tare da yin kira a gare su da su yi amfani da bikin wajen nuna hadin kai, kishin kasa, zaman lafiya da mutunta juna.

Ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali muhimman sharudda ne wajen samun ci gaban kasa, inda ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi koyi da wadanda suka kafa kasar wajen nuna kaunar ta.

“Yayin da muke bikin cikar shekaru 66 da samun ’yancin kanmu, ya kamata mu rika tuna cewa akwai fata ga kasarmu, kuma bambancin da ke tsakaninmu shi ne karfinmu. Haka kuma, jajircewarmu ta bai daya ita ce ginshikin da za a gina kasa mai karfi da wadata a kai.”

Ministan ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa Gwamnatin Tarayya na ci gaba da kokarin karfafa tsaron kasa, inganta lafiyar jama’a da samar da yanayin da ’yan kasa za su iya rayuwa, aiki da kuma neman halal dinsu cikin kwarin gwiwa.

Ya kuma ce shirin gwamnatin mai taken Renewed Hope Agenda zai ci gaba da kokarin samar da Najeriya mafi inganci ga dukkan ’yan kasar.

Tunji Ojo ya bukaci ’yan Najeriya da su yi amfani da bikin wajen sake tabbatar da kudurinsu na samar da hadin kan da zaman lafiya a kasa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here