Najeriya ta dakatar da yin amfani da samfurin kasashen waje da masu fasahar dora murya a talla-tallace su ke yi

ARCON
ARCON

Gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da yin amfani da samfurin kasashen waje da masu fasahar dora murya a talla-tallace su ke yi a Najeriya.

Shugaban hukumar da ke kula da tallace-tallace ta Najeriya  (ARCON), Olalekan Fadolapo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Olalekan ya ce dokar zata fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Oktuba na shekarar 2022.

Sanarwar ta kara da cewa a wani yunkuri na habbaka fasahar masu dora murya na gida, ya zama dole a hana amfani da na kasashen waje, domin yin haka zai habbaka fasahar tasu da kuma tattalin arzikin kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here