Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce an kama mutane sama da 380 da ake zargi da aikata laifuffuka, yayin da aka samu nasarar yanke wa fiye da 230 hukunci cikin watanni biyu na fara tsaurara matakan yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da safararsu ba bisa ka’ida ba a jihar.
Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya, wanda aka gudanar a filin wasanni na Sani Abacha da ke Kano.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya ce gwamnatin jihar ta kafa rundunar hadin gwiwar hukumomi daban-daban Kano State Multi-Agency Task Force on Drug Abuse and Illicit Trafficking a watan Yulin 2026.
Ya ce gwamnatin ta kuma bada da wani umarnin zartarwa domin karfafa yaki da haramtattun kwayoyi, daba da sauran laifuffukan da ke da alaka da su.
Read also: Duk da umarnin kotu, NNPP ta ce rushe kwamitocin zartarwa na Kano ya nan daram
A cewarsa, tun bayan kafa rundunar, ta yi nasarar tarwatsa wuraren saye da shan miyagun kwayoyi tare da lalata maboyar masu aikata laifuffuka a sassa daban-daban na jihar.
Gwamna Yusuf ya bayyana yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi da aikata laifuffuka a matsayin nauyin da ya rataya a wuyan kowa, ciki har da gwamnati, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, al’umma, iyaye da sauran jama’a.
Ya bukaci matasa da su guji miyagun kwayoyi, tashin hankali da aikata laifuffuka, tare da rungumar ilimi, noma, fasahar zamani, sana’o’i da masana’antun kirkire-kirkire.
Read also: Najeriya Ta Zama Ta Daya A Jerin Kasashen Da Suka Fi Kowacce Kasa Rashin Matsuguni A Afrika
Gwamnan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro, karfafa tattara bayanan sirri daga al’umma da kuma magance matsalolin zamantakewar da ke haddasa aikata laifuffuka da rashin tsaro.
Ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau da tsaro, inda matasa za su iya gudanar da sana’o’insu tare da ba da gagarumar gudummawa wajen ci gaban Jihar Kano.













































