Tinubu ya yi tsokaci kan dawowa da tallafin man fetur, yayin da farashin mai ke ci gaba da tashi

Tinubu Tinubu drugs 680x430

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi watsi da yiwuwar dawo da tsarin tallafin man fetur a Najeriya, inda ya yi gargaɗin cewa bai kamata a janye gyare-gyaren tattalin arzikin da gwamnatinsa ta fara ba, yana mai bayyana kiraye-kirayen yin hakan a matsayin “waƙar ruɗin kai”.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabinsa na ranar ’yancin kai ga ’yan Najeriya a ranar Alhamis, yayin da ƙasar ke bikin cika shekaru 66 da samun ’yancin kai, inda ya kare gyare-gyaren da gwamnatinsa ta aiwatar tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Shugaban ƙasar ya ce gwamnatinsa ta zaɓi fuskantar matsalolin da suka daɗe suna addabar tattalin arzikin ƙasar, maimakon ci gaba da aiwatar da manufofin da ke rage radadin matsalolin kawai.

“Gyare-gyarenmu ba su ne suka haifar da raunin da tattalin arzikinmu yake da shi ba. Sun fuskance su ne,” in ji Tinubu.

“Dole ne mu yi watsi da kiraye-kirayensu na ruɗarwa”

Tinubu ya ce gyare-gyaren sun kasance masu wahala, tare da amincewa cewa tasirinsu ga jama’a ya kasance na gaske, amma ya kafa hujjar cewa watsi da su zai zama komawa ga tsofaffin manufofin da suka gaza magance matsalolin da suka shafi tushen tattalin arzikin ƙasar.

Ya yi gargaɗi kan kiraye-kirayen da wasu manyan mutane masu tasiri, waɗanda ya bayyana a matsayin masu goyon bayan koma-baya, ke yi na a yi watsi da gyare-gyaren tare da dawo da tsarin tallafin man fetur.

“Yanzu, yayin da wasu manyan mutane masu tasiri amma waɗanda ke goyon bayan koma-baya suke son mu yi watsi da kokarinmu, mu koma ga shaye-shayen tallafin da muka saba da su, dole ne mu yi watsi da kiraye-kirayensu na ruɗarwa,” in ji shugaban ƙasar.

“Dole ne mu tuna dalilin da ya sa muka fara wannan tafiya da kuma irin nisan da muka riga muka yi.”

Tinubu ya kwatanta halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki kafin gyare-gyaren da yanayin majiyyacin da ke fama da cutar daji, wanda jinyarsa ke da zafi amma wajibi ce, yana mai cewa gwamnatocin baya sun fi mayar da hankali kan rage radadin matsalolin maimakon magance su daga tushe, lamarin da ya ba su damar ƙara ta’azzara.

“Likitan majiyyacin ya bayyana masa cewa jinyar za ta kasance mai wahala da zafi, amma akwai kyakkyawar damar warkewa. Majiyyacin yana da zaɓi. Zai iya fara jinya, ya jure radadinta tare da yaƙar cutar. Ko kuma ya nemi kawai a ba shi maganin rage zafi, ya rage jin radadin tare da barin cutar dajin ta ci gaba da yaɗuwa.

“Na tsawo lokaci, shugabannin Najeriya sun zaɓi maganin rage zafi, suna addu’ar samun wata mu’ujiza da ba ta taɓa zuwa ba,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya lissafa nasarorin tattalin arziki

Yayin da yake kare gyare-gyaren, Tinubu ya ce yanayin tattalin arzikin Najeriya ya inganta, inda ya ambaci samun ci gaban tattalin arziki da ya haura kashi huɗu cikin ɗari a shekarar 2026, tare da gudummawar ɓangaren mai da sauran sassan tattalin arzikin da ba na mai ba.

Ya kuma ce satar ɗanyen mai ta ragu, hauhawar farashin kayayyaki ta sauka sosai daga matakin da ta kai a baya, an sake gina ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje, kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje ta samu daidaito.

Shugaban ƙasar ya ce Najeriya ta samu kuɗaɗen shiga sama da dala biliyan shida daga fitar da kayayyakin da ba na mai ba zuwa ƙasashen waje a shekarar 2025, wanda ya bayyana a matsayin mafi girma a tarihin ƙasar.

“Waɗannan ba iƙirari ne marasa tushe ba. Masu sa ido na ƙasashen duniya, ’yan jarida, ƙungiyoyi masu zaman kansu da cibiyoyin haɗin gwiwar ƙasashe da dama suna iya ganin sauyin,” in ji shi.

“Dukkansu sun tabbatar da cewa gyare-gyarenmu sun ƙarfafa daidaiton tattalin arzikin Najeriya da kuma juriyarsa wajen fuskantar matsaloli. Kamfanoni masu zaman kansu sun riga sun bayyana matsayinsu, yayin da jarin kai tsaye daga ƙasashen waje ke ci gaba da ƙaruwa a kowace shekara.”

Tinubu ya ce ƙasar ta kai wani muhimmin mataki na sauyi, inda gwamnati yanzu ta fara sauya akalar ayyukanta daga gyara tattalin arziki zuwa mayar da hankali kan samar da ayyukan yi, haɓaka samar da kayayyaki da bunƙasa walwalar jama’a baki ɗaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here