Manjo janar Abubakar ya zama kwamandan rundunar Operation Hadin Kai

FB IMG 1745907585263 750x430

Manjo janar Abdulsalam Abubakar ya zama kwamandan runduna ta 15, a rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) da ke Arewa maso Gabas.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Abubakar ya gaji Manjo janar Waidi Shaibu.

NAN ta kuma ruwaito cewa, Abubakar, wanda ya karbi ragamar mulki daga hannun magabacinsa a wani bikin mika ragamar mulki a hedikwatar rundunar da ke Maiduguri, ya kasance har zuwa sabon nadin nasa, mataimakin kwamandan kuma darakta na nazari a kwalejin tsaro ta kasa da ke Abuja.

Ya taba rike mukamin Kwamanda sashi na 3 na OPHK da Multinational Joint Task Force a Monguno da Kwamandan shiyya ta 1 OPHK Maiduguri da sauran mukamai.

Karin karatu: Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele kan dawo masa da gidajen da EFCC ta ƙwace guda 753 a Abuja 

A jawabinsa na bankwana, Shaibu ya godewa jami’an hukumar bisa goyon baya da hadin kai da suka ba shi a zamaninsa.

Ya bayyana lokacin da ya kasance a cikin rundunar a matsayin tafiya mai cike da ayyuka masu yawa a yankunan ‘yan ta’adda, yana mai jaddada mahimmancin ci gaba da kwarewa da sadaukar da kai don girmama jaruman da suka mutu.

Ya bukaci sojojin da su mika biyayya da goyon bayansu ga magajinsa, wanda ya bayyana a matsayin jigo a aikin yaki da ta’addanci a rundunar. (NAN) (www.nannews.ng)

HMS/DCO

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here