Har yanzu Burkina Faso ba ta saki jirgin C-130 da ta kwace ba, tare da tsare sojoji 11 – Gwamnatin Tarayya 

File photo of C 130 aircraft

Gwamnatn tarayya ta bayyana cewa ana ci gaba da  tattaunawa kan tsare jirgin Rundunar Sojin Sama na Najeriya samfurin C-130 da kuma sojoji 11, inda ta ce har yanzu gwamnatin Burkina Faso ba ta sakesu ba.

Idan za a iya tunawa, an kwace jirgin tare da ma’aikatan jirgi da sojojin da ke cikinsa ne a ranar Litinin, jim kaɗan bayan jirgin ya sauka a Bobo Dioulasso da ke Burkina Faso a matsayin matakin kariya.

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta bayyana cewa jirgin yana kan hanyarsa zuwa ƙasar Portugal domin aikin gyara, inda ya sauka sakamakon matsalar fasaha da ta taso a hanya.

Sai dai gwamnatin Burkina Faso tare da takwarorinta a ƙungiyar ƙasashe yankin Sahel sun zargi ma’aikatan jirgin da shiga sararin samaniyarta ba tare da izini ba, abin da ya sa aka tilasta saukar jirgin.

A kan wannan lamari, kakakin ma’aikatar harkokin waje Mr Kimiebi Ebienfa ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da hulɗa da hukumomin ƙasar da abin ya shafa domin warware matsalar ta hanyar diflomasiyya, amma har yanzu ba a saki jirgin da sojojin ba.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar harkokin waje ce ke jagorantar tattaunawar domin tabbatar da sakin jirgin da kuma lafiyar dakarun Najeriya, lamarin da ya sa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta ɗauki matakin yin shiru kan batun a halin yanzu.

Ta kuma fahimci cewa Burkina Faso da kasashen yankin Sahel kamar Mali da Nijar, waɗanda a baya mambobi ne na Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS kafin dakatar da su sakamakon juyin mulki, na ƙoƙarin amfani da lamarin a matsayin hanyar matsin lamba, bisa la’akari da tasirin takunkumin kasuwanci da motsi na kaya da ayyuka da ya jefa su cikin matsin tattalin arziki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here