Tinubu ya amince da karin matsayi na musamman ga ADC dinsa, kasa da shekara guda bayan daga shi zuwa matsayin Kanal

Aide de Camp to the President Nurudeen Yusuf being decorated colonel by President Tinubu in January 2025 750x430 (1)

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da karin matsayi na musamman na ga mataimakinsa na soja Aide-de-Camp, Nurudeen Yusuf, daga mukamin Kanal zuwa Birgediya Janar, duk da cewa bai kai shekara guda da ɗaga shi zuwa Kanal ba.

Naɗin nasa na cikin wata wasika daga ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro zuwa ga babban hafsan sojin ƙasa.

Kafin fitar da takardar tana da dauke da sa hannu na ranar 12 ga Disamba 2025 da Nuhu Ribadu ya rattaba hannu a kai.

A cikin wasikar, an bayyana cewa duk da karin matsayin da aka yi wa Nurudeen Yusuf, zai ci gaba da rike mukaminsa na ADC ga shugaban ƙasa ba tare da sauyi ba, tare da aiwatar da karin mukamin daga ranar da aka amince da shi.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki ya janyo ce-ce-ku-ce a Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, inda wasu jami’ai ke nuna rashin jin daɗi bisa abin da suke kallon fifiko da karya ƙa’idojin tsarin karin mukami a rundunar soji.

A karkashin ƙa’idojin rundunar soji, ana bukatar Kanal ya cika wasu sharudda kafin daga shi zuwa Birgediya Janar, ciki har da kammala karatu a makarantar yaƙi ko kwas na manyan jami’ai, da kuma karatun dabarun tsaro a Kwalejin Tsaron Ƙasa ko makamancinta, tare da shafe akalla shekaru hudu zuwa biyar a matsayin Kanal.

Haka kuma an nuna cewa Nurudeen Yusuf an daga shi zuwa Kanal ne a watan Disambar 2024, sannan Shugaba Tinubu ya masa ado da mukamin a watan Janairu 2025 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, bayan an naɗa shi ADC tun watan Afrilu 2023 kafin rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.

Masu sharhi kan harkokin jama’a sun bayyana cewa irin wannan karin mukami cikin gaggawa na iya lalata tsarin kwarewa, bin ka’ida da martabar rundunar soji, tare da janyo raunin kwarin gwiwa a tsakanin jami’an da suka bi dukkan matakan da doka ta tanada kafin samun irin wannan matsayi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here