Abuja: An kai wa wata mai juna biyu hari tare da sanya mata hayaƙi mai sa hawaye, yayin da jami’an hukumar FHA da ‘yan sanda dauke da makamai suke rushe kadararta bayan lamarin na gaban kotu

WhatsApp Image 2025 12 15 at 08.44.25 750x430

Darakta janar na hukumar kula da gidajen gwamnatin tarayya, Oyetunde Ojo, ya aike da motoci biyu dauke da ‘yan sanda masu makamai domin rusa wata kadara a birnin Abuja, duk da cewa shari’ar gidan tana gaban kotu.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan sandan tare da wasu ma’aikatan hukumar sun isa wurin a tsakar rana ranar Juma’a, inda aka zargi sun kai wa mai kadarar hari, wadda ke dauke da juna biyu, ta hanyar dukan ta da jan ta a kasa yayin da ta yi kokarin hana rushe kadarar.

Kadarar na kan titin Avenue na biyar, titinai lamba 52, a yankin rukunin gidajen da ke Gwarinpa a birnin Abuja, kuma mallakar kamfanin Tolwu Integrated Properties Limited ce.

Mai kadarar, Hajiya Sadiya, ta bayyana cewa an doketa, an ja ta a kasa kuma ta samu rauni a hannunta, inda ta ce hakan ya faru ne duk da cewa shari’ar tana gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Bwari, wadda ta bayar da umarnin a ci gaba da kasancewa a halin da ake ciki har sai an kammala shari’ar.

Da yake yiwa manema labarai karin bayani, Hajiya Saudiya, ta ce tawagar ‘yan sandan da ta je wurin karkashin jagorancin mataimakiyar shugaban hukumar FHA Madam Funmi, ba su gabatar da wata takardar kotu ko izinin aiwatar da hukunci ba duk da bukatar hakan.

Karanta: Tinubu ya amince da karin matsayi na musamman ga ADC dinsa, kasa da shekara guda bayan daga shi zuwa matsayin Kanal

Ta ce, lamarin da ya kai ga amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye a kanta, tare da kama mijinta aka kai shi ofishin ‘yan sanda na Gwarinpa.

Hajiya Sadiya ta ce ta sayi filin ne tun shekarar 2012, ta kuma samu takardar amincewa daga hukumar FHA bayan ta biya dukkan basussukan da ake binsa, sannan daga baya aka amince da canjin manufar amfani da filin da kuma tsarin gini bayan cika dukkan sharuddan da hukumomin suka tanada.

Ta bayyana cewa matsalar ta fara ne bayan sabon shugaban hukumar FHA ya yanke wani bangare na filin ba bisa ka’ida ba ya ba wani kamfani, lamarin da ya sa ta garzaya kotu bayan barazana da cin mutunci da aka yi mata, yayin da wasu ma’aikata da masu ruwa da tsaki a hukumar suka bukaci a binciki zargin cin hanci, amfani da ofis ba daidai ba da kuma karkatar da bayanan filaye a hukumar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here