2026: Hukumar kiyaye hadura ta kasa ta fara shirin aikin daukar ma’aikata

FRSC Shehu Mohammed sabo 750x430 (1)

Hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) ta sanar da shirinta na fara daukar ma’aikata aiki na 2026, inda take gayyatar ‘yan Najeriya da suka cancanta su nemi aiki a matakai na hukumar, wanda suka hada da Marshal Inspectorate da Road Marshal Assistant Cadres.

A cewar sanarwar daukar ma’aikatan da aka fitar a ranar Alhamis kuma Pauline Olaye, Deputy Corps Marshal, shugabar gudanarwa da kula da ma’aikata ta sanya wa hannu. Ta ce an bude daukar aikin ne ga masu sha’awa kuma wadanda suka cancanta da ke neman aiki a sassa daban-daban na hukumar, yayin da take ci gaba da kara karfin ma’aikatanta da inganta hidima a fadin kasa.

Hukumar ta ce ana neman masu ma’aikatan ne a mukamai ciki har da, Superintendent Route Commander (SRC), Route Commander/Deputy Route Commander (RC/DRC), Assistant Route Commander (ARC), Marshal Inspector II da III, da kuma Road Marshal Assistant I, II da III.

FRSC ta ce masu neman aiki a matakin Officer Cadre dole ne su kasance da digirin jami’a ko babbar difiloma ta kasa (HND) daga makarantun da aka amincewa, yayin da masu neman Marshal Inspectorate da Road Marshal Assistant Cadre dole ne su cika ka’idojin ilimi da kwarewa na dukkan matakan da suke nema..

Hukumar ta bayyana cewa masu sana’o’i, direbobi da matuka babur masu cancanta da kwarewa ma za su iya nema a matakin Road Marshal Assistant.

Ta kara da cewa masu neman dole ne su kasance ‘yan Najeriya ta hanyar haihuwa, masana aiki da na’ura mai kwakwalwa kuma lafiyayyu, yayin da samun ingantaccen shaidar tuki zai zama wani karin daraja ga masu neman aikin.

Sauran bukatun sun hada da samun takardar shedar lafiya daga asibiti da gwamnati ta amince da shi, lasisin kwarewa da suka dace a inda ake bukata da kuma cika mafi karancin tsawo na mita 1.65 ga maza da mita 1.58 ga mata.

Hukumar ta kara da cewa masu neman aikin dole ne su kasance da hali mai kyau, marasa almubazzaranci kuma ba a taba yanke musu hukuncin wani laifi ba.

FRSC ta ba masu son nema shawara su mika aikace-aikacen su ta yanar gizo ta hanyar shafinta na daukar ma’aikata: https://t.co/j7cYJ1OkLf.

Hukumar ta ce dole ne a mika aikace-aikace cikin makonni 4 daga ranar Juma’a, 3 ga Yuli, 2026, inda ta jaddada cewa daukar ma’aikatan kyauta ne.

Ta yi gargadin masu nema su yi hattara da masu zamba kuma ta sake jaddada cewa ba a bukatar biyan kudi a kowane mataki na aikin daukar ma’aikata.

Don tambaya, hukumar ta umurci jama’a su tuntubi lambar taimako: 122.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here