Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai wata ziyarar bazata wasu asibitoci guda biyu a Maiduguri, da karfe 10 na daren jiya Juma’a, sai dai ya tarar da marasa lafiya a cikin duhu sakamakon rashin wutar lantarki da aka kwashe tsawon kwanaki.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Zulum yakai ziyara asibitin Umaru Shehu Ultra Modern Hospital da Fatima Ali Sheriff Maternity Hospital, dukkansu a kusa da al’ummar Bulumkutu da ke Maiduguri.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Malam Isa Gusau, ya fitar a ranar Asabar, ta ce Zulum ya dawo daga Abuja ne ya yanke shawarar tashi daga filin jirgin kai tsaye zuwa asibitoci, jim kadan bayan da wasu majiyoyi masu zaman kansu suka bayyana cewa asibitocin na cikin tsabar duhu.
Sanarwar ta ce, dukkanin asibitocin biyu sun dogara ne da injinan janareta, saboda rashin samun wutar lantarki daga cibiyar lantarkin ta kasa, tun bayan da kungiyar Boko Haram ta lalata kayayyakin wutar da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, inda har yanzu jami’an gwamnatin tarayya da na jihar ke ci gaba da kokarin dawo da hanyoyin sadarwa. zuwa yankunan da har yanzu ba su sami wutar lantarki ba, ciki har da sassan Bulumkutu.
“Idan za mu iya kunna fitulunmu a koyaushe akan tituna, ban ga dalilin da zai sa ba za mu iya ba da wutar lantarki acikin asibitocinmu ba” Inji zulum
Daganan Zulum ya koka yayin da yake jajantawa marasa lafiya da ‘yan uwansu saboda kasancewa cikin duhu duk da fama da cututtuka.
A wani mataki na tabbatar da dorewar wutar lantarki a asibitocin biyu, Gwamna Zulum a daren jiya ya ba da umarnin inganta na’urorin da ke amfani da hasken rana a asibitin mata na Fatima Ali Sheriff.