Dan takarar majalisar wakilai na Jam’iyyar PDP a Osun ya rasu

PDP PDP
PDP PDP

Dan takarar jam’iyyar PDP mai wakiltar mazabar Irewole-Isokan-Ayedaade a jihar Osun a zaben 2023 Sola Arabambi ya rasu.

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar, tsohon dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Osun, Prince Dotun Babayemi ya ce mutuwar Arabambi ta razana mutane da dama, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai gaskiya.

Wani mataimaki ga marigayi Arabambi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce shugaban nasa ya rasu ne bayan fama da wata gajeriyar jinya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Hakika labarin rasuwar Sola ya zo min da bazata. Mutum ne mai hidima.

Da yake jajantawa ‘yan uwa da jam’iyyar da kuma al’ummar mazabar tarayya bisa rasuwar, Babayemi ya yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here