Tsohon fitaccen dan jarida kuma manazarci mai gidajen rediyo da talabijin da dama, Bashir Mohammed Baba ya rasu.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Bashir Baba ya rasu a safiyar yau Asabar a Abuja.
Rahotanni sun ce ya rasu ne da sanyin safiyar yau sakamakon raunukan da ya samu a cikin bandakinsa.
Bashir Baba gogaggen dan jarida ne sama da shekaru arba’in wanda ya fara aiki da NTA, manazarci ne a BBC, VOA, DW-Radio da kuma Prestige Radio dake Minna, shirin ‘Kasar Mu a Yau’ da kuma shirin Idon Mikiya na Farin Wata Television/Vision FM
Ya fara shirye-shiryen kasar mu ayau a Liberty Television. Ya kuma kasance Babban Mataimakin Mai Watsa Labarai (Ma’aikatar Harkokin Waje) a karkashin Ambasada Aminu Bashir Wali.













































