Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar Sallah ga Alhazan jihar a masaukinsu da ke kasar Saudiyya, inda ya bai wa kowane mahajjaci kyautar Riyal 250, kwatankwacin Naira 105,000.
Gwamnan ya kai ziyarar ne a daren ranar Asabar.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yaba da nasarar aikin Hajjin bana da aka samu, inda ya bayyana shi a matsayin wanda ya fi na shekarun baya, musamman na bara.
”Aikin Hajjin bara ma ya yi kyau, duk da haka, wannan ya fi kyau, kuma muna godiya ga Allah da wannan nasarar,” inji shi.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, gwamnan ya bayyana cewa ziyarar na da nufin karfafa alaka da yin addu’o’i ga jihar Kano da Najeriya, da kuma mika gaisuwa ga mahajjata a bikin Sallah.
“Kano da Najeriya ma suna bukatar addu’a, kuma ina rokon ku da ku yi musu addu’a da kuma wadanda suka mutu a lokacin atisayen,” in ji shi.
Gwamnan ya jajanta wa iyalan mahajjatan da suka rasa rayukansu a Makkah da Madina, da kuma lokacin Arafah, inda ya yi addu’ar Allah ya jikan da wadanda suka rasu.
Ya kuma bukaci alhazai da su ci gaba da gudanar da ibada tare da kaurace wa duk wani abu da zai kawo cikas ga aikin Hajjin nasu.
Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga hukumar alhazai ta Kano da sauran masu ruwa da tsaki da suka bayar da gudumawa wajen gudanar da aikin Hajjin cikin sauki.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah ya karbi aikin Hajjin Alhazai ya kuma dawo da su Najeriya lafiya.
Shi ma da yake nasa jawabin babban Daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, Lamin Rabi’u Danbaffa, ya nuna jin dadinsa ga gwamnan bisa irin goyon baya da kokarin da ya yi a yayin gudanar da aikin hajjin.













































