Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta ce ta fara bincike kan wasu dubun dubatar kuɗaɗen ƙasar waje da aka kama a filin jirgin sama na Kano.
Jaridar solacebase ta rawaito cewa, EFCC ta ce an ga dala 86,500,305 da kuma riyal 305,150 ne cikin wata jaka lokacin da aka ga wani ma’aikacin filin jirgin mai suna Sale Bala ya yi yunƙurin ɗaukar ta ranar Lahadi.
Har ma EFCC ta yi zargin cewa, kudaden an shigo da su ta barauniyar hanya, kuma an kama su ne a ranar 27 ga watan Afrilun 2025.
Karin karatu: Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele kan dawo masa da gidajen da EFCC ta ƙwace guda 753 a Abuja
“Bayan bincike, jami’an kwastam sun gano kuɗaɗen ne da aka ɓoye cikin zannunwan gado,” in ji EFCC cikin wata sanarwa.
“An kama Sale Bala da wani Abdullahi Tahir da ake zargin shi ne aka tsara zai karɓi jakar bayan kammala tantance ta.”
Ta ƙara da cewa kuɗin da kuma waɗanda ake zargi na tsare a hannunta, kuma EFCC za ta kai su kotu da zarar an kammala bincike.