Jam’iyyar ADC ta sanar da jadawalin gudanar da zabukan cikin gida a fadin kasa gabanin babban taron jam’iyyar na kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga Afrilu, 2026.
Sanarwar jama’a ta samu sa hannun sakataren tsare-tsare na kasa, Prince Chinedu Idigo, da sakataren yada labarai na kasa, Mallam Bolaji Abdullahi.
Sanarwar ta bayyana cewa za a gudanar da zabukan matakin rumfunan zabe da na gundumomi a ranar 7 ga Afrilu, 2026, sannan a bi da zabukan kananan hukumomi a ranar 9 ga Afrilu, yayin da zabukan jihohi za su gudana a ranar 11 ga Afrilu.
Ta kuma bayyana cewa wannan tsari zai kare ne da babban taron jam’iyyar na kasa da aka tsara gudanarwa a ranar 14 ga Afrilu, 2026.
Jam’iyyar ta shawarci mambobin da ke da sha’awar neman mukamai da ba su da masu rike da su da su karba tare da cike fom din tsayawa takara ko na nuna sha’awa ta shafin internet na hukuma na jam’iyyar ADC.
Sanarwar jadawalin ayyukan zabukan cikin gida na shekarar 2026 da babban taron jam’iyyar ta bayyana cewa wannan tsari na daga cikin nauyin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya dora mata na sabunta tsarin shugabanci a dukkan matakai na jam’iyyar, tun daga rumfunan zabe da gundumomi zuwa kananan hukumomi da jihohi, kafin a kammala da babban taron jam’iyyar na kasa.
Jam’iyyar ta kuma bukaci dukkan mambobinta a fadin kasa su shiga cikin wannan tsari da himma tare da gudanar da kansu bisa kundin tsarin mulki, ka’idoji da kuma dabi’un dimokuradiyya na jam’iyyar ADC.
Jam’iyyar ADC ta fitar da wannan jadawali ne bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta sake fasalin jadawalin zabukan gama gari na shekarar 2027 bayan kafa dokar zabe ta shekarar 2026.
A karkashin sabon jadawalin, za a gudanar da zabukan shugaban kasa da na majalisar dokokin kasa a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da zabukan gwamna da na majalisar dokokin jihohi za su gudana a ranar 6 ga Fabrairu, 2027, duka kafin lokacin da aka tsara a baya domin kauce wa karo da azumin watan Ramadan.
An tsara zabukan fidda gwani na jam’iyyun siyasa tsakanin ranar 23 ga Afrilu zuwa 30 ga Mayu, 2026, yayin da dole jam’iyyun siyasa su mika sunayen ‘yan takararsu daga ranar 27 ga Yuni zuwa 11 ga Yuli, 2026. Za a fara yakin neman zabukan kasa a ranar 19 ga Agusta, 2026, yayin da za a fitar da rijistar masu kada kuri’a a ranar 15 ga Disamba, 2026.













































