Rikicin ƙarancin abinci na shirin kunno kai a Arewa sakamakon ayyukan ƴan bindiga – Bafarawa

Attahiru Bafarawa
Attahiru Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, kuma mamba a kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa, a ranar Lahadi, ya nuna damuwarsa kan ayyukan ƴan bindiga a yankin Arewa-maso-Yamma da kuma Arewa-maso-Gabas, inda ya bayyana fargabar cewa hakan ka iya haifar da matsalar karancin abinci.

A cewarsa, ya kamata sabuwar gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dauki batun samar da abinci a matsayin daya daga cikin abubuwan da ta sa gaba.

Bafarawa ya kuma yi gargadin cewa idan ba a dauki tsauraran matakai na dakile tashe-tashen hankula ba, Arewa za ta fuskanci koma bayan ilimi mai tsanani.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar PUNCH a jiya Lahadi.

Bafarawa ya ce, “Maimakon maganar naɗin ministoci, tallafin mai da kuma tattalin arziki, kamata ya yi gwamnati ta yi la’akari da batun samar da abinci domin a halin da muke ciki, nan da watanni uku masu zuwa, tabbas za mu fuskanci matsaloli a Najeriya, musamman a Arewa-maso-Yamma.

“’Ƴan bindiga sun ki barin manoma su yi noma. Wannan lamari dai ya na da matukar hadari, ba wai kawai yan bindigar na kashe mutane ba, har ma da karancin abinci zai yi tsanani nan da wasu watanni masu zuwa, musamman a yankin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas. Don haka mu na son gwamnati ta farka ta yi wani abu a kai,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here